Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Jaridar Faransa Da Aka Sace A Mali Ya Nemi Taimako A Bidiyo


Dan jaridar kasar Faransa da aka yi garkuwa da shi
Dan jaridar kasar Faransa da aka yi garkuwa da shi

Wani dan jaridar Faransa da ‘yan tawaye suka sace a garin Gao da ke arewacin kasar Mali a watan jiya ya bayyana a cikin wani bidiyo, inda yake rokon hukumomin Faransa da su yi duk abin da za su iya don ceton sa.

“Ni ne Olivier Dubois. Ni Bafaranshe ne kuma dan jarida ne. JNIM (ƙungiyar da ke da alaƙa da al-Qaeda) ne suka sace ni a Gao ranar 8 ga Afrilu. Ina kira ga iyalai na, abokaina da hukumomin Faransa don su yi duk abin da za su iya su ‘yantar da ni,” in ji Dubois a cikin bidiyo na sacan 21 da aka yada a shafukan sada zumunta.

Ba a dai tabbatar da sahihancin bidiyo ba nan take.

Wata majiyar ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar da bacewar dan jaridar kuma ta ce ma’aikatar tana kan magana da danginsa tare da gudanar da bincike na fasaha kan sahihancin bidiyon.

Kawo yanzu, ba a samu bayanai daga hannun hukumomin Mali ba.

Dubois shi ne Bafaranshe na farko da ‘yan tawaye suka yi garkuwa da shi a Mali tun bayan da aka sako‘ yar aikin sakai ta Faransa, Sophie Petronin a watan Oktoban bara. An sace ta ne a kusa da Gao a ƙarshen 2016.

XS
SM
MD
LG