Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dauki Matakan Samar Da Tsaro Da Zaman Lafiya A Agadez


Sojan Jamhuriyar Nijar a Agadez

Kwamitin samar da zaman lafiya a yankin Agadez na kasar Jamhuriyar Nijar, ya dauki matakan gaggawa domin daukaka sha’anin tsaro a yankin dake fama da tashin hankali.

A zaman da kwamitin tsaron yayi da wasu kungiyoyin farafen hula, sun yanke shawarar matakan da suka hada da binciken kwakwaf akan duk wata mota dake yawo ba tare da lamba ba, tare da sintirin jami’an tsaro a kowanne lokaci, haka kuma za a rika dakatar da bincikar duk wata mota dake yawo da bakaken gilashi da kuma bincikar duk gidan da aka zargi ana ajiye makamai cikin sa.

Wasu daga cikin al’umar Agadez, sun nuna farin cikinsu ga wadannan matakai da aka dauka inda suke ganin tabbas wadannan matakai zasu taimaka wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da ya dade yana fama da tashin hankali.

Sai dai wasu kungiyoyin farafen hula na ganin wadannan matakai da aka dauka sun zamanto tamkar ihu ne bayan hari. A cewar Saleh Mamba na gamayyar kungiyoyin fararen hula, dole ne sai hukumomi sun hada kai da al’umomin yanki idan ha rana son tabbatar da tsaro. Ya kuma ce dole ne sai an ajiye jami’an tsaron sirri na din din din.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

XS
SM
MD
LG