Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Fitar Da Rahotan Dake Nuna Shugaba Jacob Ya Aikata Rashawa A Afirka Ta Kudu


Masu goyon bayan Shugaba Zuma yayi Murabus
Masu goyon bayan Shugaba Zuma yayi Murabus

Alkali a Kasar Afirka ta Kudu yaba da Umarni a bayyana takardun rahoton dake dauke da zargin aikata Rashawa da ake yiwa shugaban Kasar Jacob Zuma nan take.

Umarnin ya fito ne bayan Zuma ya hana bayyana rahoton da masu kare Al’umma suka bayar, Manyan Jami’an kare Rashawa na Afirka ta Kudu.

Rahoton dai na nuna yadda Zuma yabar zuri’ar Gupta masu karfin arziki suka taka rawa a gwamnatin sa. Ana zargin shugaban yabaiwa Iyalin na Gupta damar zaben wasu daga cikin ministocinsa.

A baya za a bayyana rahoton ne a watan da wuce kafin Zuma ya hana.

Tuni dai Zuma ya fuskanci kakkausan kalubale na yin amfani da kudi kimanin Dalar Amurka Miliyan 20 na kudin kasa domin gyaran gidansa dake wajen gari. Inda daga baya ya nemi afuwa sannan ya yarda zai maida wani kaso daga cikin kudaden

Dubun nan Yan Afirka ta Kudu ne suka fita zanga zanag a babban birnin kasar wato Pretoria a ranar Laraba, suna bukatar Zuma ya sauka daga kan Mulki.

XS
SM
MD
LG