Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Mutumin Da Ya Kai Hari Da Mota A Birnin London


Ma'aikatan gaggawa a London
Ma'aikatan gaggawa a London

'Yan sandan yaki da ta’addanci a Birtaniya sun ce sun gano asalin mutumin nan da aka kama a jiya Talata bayan ya abka da mota a cikin tarin jama’a masu tafiyar kasa da masu amfani da kekuna a wajen harabar majalisar dokokin kasar dake birnin London.

Sai dai kuma hukumomin basu bayyana ainihin sunan mutumin ga jama’a ba, koda yake dai sun ce dan shekaru 29 ne kuma dan kasar Birtaniya ne mai asali daga Sudan.

Yanzu haka dai ana tsare da shi ne a kan zaton aikata ta’addanci da kuma yunkurin aikata kisa.

'Yan sanda sun fada a yau Laraba cewa abin da binciken ya maida hankali akai shine, gano dalilin kai wannan hari da ya jikata mutane uku. An kai mutane biyu a cikin wadanda suka ji raunin zuwa asibiti domin duban lafiyarsu kuma tuni aka sallamesu.

Frai ministan Birtaniya Theresa May ta rubuta a shafinta na Twitter, tana jajantawa wadanda suka ji rauni, kana ta godewa ma’aikatan ceto da suka yi gaggawar kai dauki.

Shima Shugaban Amurka Donald Trump ya yi tsokaci a kan wannan hari a wani sakonsa na Twitter yana mai cewar, an sake aikata ta’addanci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG