Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chadi: An Kaiwa Rundunar Kwantar Da Tarzoma Ta Majalisar Dinkin Duniya Hari


Wata kungiyar ‘yan ta’adda mai alaka da al-Qaida a jiya Lahadi ta dau alhakin kai hari a kan sansanin rundunar kwantar da tarzoma ta Majalisar Dinkin Duniya da aka kai a arewacin Mali a jiya Lahadi, harin da ya kashe sojojin zaman lafiya daga Chadi guda goma kana ya jikata wasu 25.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da harin kuma ya kira harin da aikata laifin yaki.

Mai Magana da yawun Guterres ya aike da ta’aziyarsa ga gwamnati da mutane kasar Chadi da kuma iyalan sojojin da harin ya rutsa dasu. Ya kuma yabawa sojojin maza da mata da suka yi tsayi daka a fagen daga, suka kuma sadaukar da rayuwarsu a cikin hatsari.

Kungiyar al-Qaida na yankin Maghreb tana ci gaba da daukar alhakin harin. Ta kuma ce harin martani ne ga sabon kulla huldan diflomasiya da Chadi ta yi da Isra’ila.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG