Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutum 9 A Myanmar A Cewar Kungiyar Taimaka Wa Fursunonin


A cigaba da kazancewa da dambarwar siyasar Myanmar ke yi, a jiya Alhamis an kashe mutane 9 a Myanmar, a cewar rahoton da kungiyar taimaka wa fursunonin siyasa ta bayar. 

Kwana daya bayan zaman gida da suka yi a ranar Laraba, wanda kusan ya mayar da tituna wayam a akasarin garuruwan kasar.

Rahotanni da dama na bayyana yadda sojoji suke amfani da karfi don tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Mawlamvine da Hpa-An, hedikwatar jihar Karen. Haka sojoji sun fada kan wasu da ke makokin mutuwar 'ya uwansu a fadin kasar, tare da samun rahoton wani mutum da aka bindige har lahira.

Rahoton kungiyar ta AAPP ya ce sojoji sun kashe mutane akalla 320 a lokacin gumurzun. Daya daga cikin wadanda aka kashe yarinya ce mai shekaru 7 da haihuwa, wadda aka harbe a ranar Talata, lokacin da sojoji suka kutsa kai cikin gidansu, a cewar jaridar Myanmar Now da Reuters.

An ruwaito yarinyar ta na zaune akan cinyar mahaifinta lokacin da sojojin suka shiga gidan su ka bukaci sanin ko akwai wani daga cikin iyalan da ke cikin gidan.

Uban yariyar ya amsa musu cewa eh akwai, amma sojojin suka ce yayi musu karya sai suka bude ma shi wuta inda suka harbe yarinyar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG