Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kona Gidaje da Satar Kayan Abinci


Gidajen da suka kone bayan hare-haren Boko Haram. (File Photo)

'Yan Boko Haram sun bakunci garin Alagarno a jihar Borno a Najeriya.

An kai hari garin Alagarno wanda ke cikin karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno a taraiyar Najeriya.

Harin dai ana tsanmani cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai harin inda suka kashe mutane akalla goma sha bakwai.

Bayan kisan, suna kwashewa jama'ar garin kayayakin abinci da kuma kona gidaje kimanin sittin a garin na Alagarno.

Wannan harin ba shine na farko ba amma wannan hari yafi na baya muni,wannan gari na Alagarno ba shida nisa da garin Chibok, garin da yayi kaurin suna saboda sace 'yan makaranta da akayi a garin.

Wakilin mu Ibrahim Alfa, yace kawo yanzu jami'an tsaro basu ce komai ba dangane wannan sabon harin,saboda basu sami umarni ba daga Abuja.
An kai sabon hari jihar Borno - 2'59"
XS
SM
MD
LG