Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Zanga Zangar Kin Jinin Juyin Mulki A Myanmar


Masu zanga zanga a Myanmar
Masu zanga zanga a Myanmar

Dubban mutane sun fito a fadin Myanmar a yau Lahadi domin bayyana rashin amincewar su ga juyin mulkin makon jiya da kuma neman sakin zababbiyar shugaba Aung Sang Suu Kyi, a wata zanga zanagr da ba a taba ganin ba tun bayan juyin juya hali a shekarar 2007 da ya taimakawa sauyin dimokaradiyar kasar.

A cikin wuni na biyu na zanga zangar gama gari, taron jama’a a birni mafi girma a kasar na Yangon, an ga masu zanga zangar sanye da jajayen riga da jajayen tutoci, launin jami’iyar Suu Kyi ta National League for Democracy Party (NLD).

Masu zanga zangar sun yi ihu suna fadin bamu kaunar mulkin soji! Muna son mulkin farar hula.

A yau Lahadi da ranar, gwamnatin sojan ta kawo karshen rufe hanyar sadarwar yanar gizo da ta yi da ya kara fusatar da mutane tun bayan juyin mulkin na ranar Litinin da ya gabata a kasar dake kudu maso gabashin Asia da ta fuskancin rikici sauyin mulki kana hankalin kasashen duniya ya koma kan abubuwa da suke faruwa a wurin.

Dimbin mutane daga sassa na birnin Yangon sun taru a cikin garin, suka cika tituna kana suka nufi dandalin Sule Pagoda dake tsakiyar birnin inda aka gudanar da tarukan gangami a gagarumin zanga zangar 2007 da mabiya addinin Buda suka jagoranta da wasu taruka a shekarar 1988.

‘Yan sanda dauke da makamai da sulke sun kafa shingaye amma basu yi wani yunkurin hana zanga zangar ba. Wasu masu tattakin sun baiwa ‘yan sandan furanni dake zama alamar zaman lafiya.

Suu Kyi, mai shekaru 75, tana huskantar tuhume tuhume guda shida na shiga da kaya kasar ba bisa ka’ida ba kana ana tsare da ita hannun ‘yan sanda domin gudanar da bincike kafin ranar 15 ga watan Faburairu. Lauyanta ya ce ba a bashi damar ganawa da ita.

XS
SM
MD
LG