Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Shirin Gudanar Da Taro A Kan Yanayi A Poland


Taro a kan yanayi a Poland Climate
Taro a kan yanayi a Poland Climate

Ministocin Muhalli daga kusan kasashen duniya 200 sun isa birnin Katowice na kasar Poland, domin neman hanyoyin da za a bi domin amfani da yarjejeniyar Paris ta 2015 don tunkarar sauyin yanayi.

Shugabannin kasashen duniya basu halarci taron sauyin yanayi na wannan shekarar ba, yawanci saboda tana bukakar amincewa da hanyoyin da za a bi wajen aiwatar da yarjejeniyar Paris.

Gabannin halartar ministocin, masu rajin kare muhalli daga ko’ina fadin duniya sun gudanar da wani maci a birnin na Poland ranar Asabar, domin nuna takaicinsu da kuma kira ga gwamnatoci da su tashi tsaye su kare muhalli.

“Wannan lokaci ne da zamu kare gidajenmu” abin da masu zanga-zangar ke fada a kusa da babban dakin da MDD zata gudanar da taron makonni biyu kan sauyin yanayi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG