Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Na Neman Karin Bayani Kan Kama Shugabar Huawei


China ta baiwa jakadar Amurka a Beijing takardan sammaci a jiya Lahadi domin bayyana kalubalantar kama ‘yar China nan shugaban kamfanin fasaha a Canada da Amurka ta nemi a mika matai ta domin mata shari’a a nan Amurka a kan zarginta da damfara.

China ta kira kama Meng Wanzhou babbar jami’ar kudi na katafaren kamfanin sadarwa na Huawei da mummunar al’amari kuma tana kira ga Amurka ta soke batun mikata bisa zarginta da karya dokokin Amurka da ta hana yin kasuwanci da kasar Iran.

Mataimakin ministan harkokin wajen China Le Yucheng ya gayyaci jakadar Amurka Terry Branstad ne wuni guda bayan ganawa ba jakadar Canada John McCallum domin kalubalantar kama Meng bisa bukatar Amurka a filin saukar jiragen sama a Vancuoveer a ranar daya ga watan Disamba.

Ma’aikatar harkokin wajen China ta fada a cikin wata sanarwa Le ke fadawa Branstad cewa abin da Amurka tayi babban take doka ne da kuma take ‘yancin ‘yar China nan kuma al’amarin ya yi matukar muni.

China tayi kira ga Amurka ta gaggauta daukar matakin ingata kura kuran da tayi kuma ta janye takardar kama ‘yan kasar China.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG