Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Lauyan Amurka Ya Tsame Kansa Daga Bincike Kan Rasha


Babban Lauyan Amurka Jeff Sessions

Babban atoni janar na Amurka Jeff Session, yace ya tsame kansa daga duk wani binciken zargin da ake yiwa Rasha na yin kutse a zaben Amurka wanda akayi a shekarar data gabata.

Session wanda ya gana da manema labarai bayan jaridar Washington post, ta tsegunta cewa tsohon sanatan kuma jigo a kanfe din shugaba Donald Trump a zamanin yakin neman zabe, ya tattauna da Jakadan Rasha a Amurka Sergei Kislyak, amma kuma ya danne wannan bayanin lokacin da yake gaban ‘yan majalisar dattijai domin a tantance shi kan wannan mukamin.

Tambayar da take ta jerangiya ko ita ce, ko Session yayi maganar kanfe din Shugaba Trump lokacin yakin neman zabe.?

Wannan dai yasa yanzu haka sanatocin daga jami’yyun biyu wato Republican da Democrat na cewa Session ya tsame kansa daga wannan binciken,Sai kuma a bangare guda sanatoci daga jamiyyar Democrat na kira ga Session din da yayi murabus domin ko ya shara karya a karkashin doka.

Idan da dai ba a manta ba a ranar 10 ga watan Janairu, sailin da ake zaman tantance shii Session din, Sanata Al-Franken na jamiyyar Democrat ya tambayi Sakataren Sharaar cewa me zaiyi kaddara an samu kwararan hujjojin cewa wani daga cikin tawagar kanfe din Trump ya tattauna da gwamnatin Rasha.

Ga kuma amsar da ya nbayar’’Gaskiya ni bansan wani batu ko lamari game da wannan ba, illa iyaka dai an bukace ni domin na maye gurbi a lokacin kanfe din kuma ni ban samu lokacin yin hakan ba, banyi maganada kowa ba daga Rasha’’

A jiya dai sailin da ya amsa wasu tambayoyin manema labarai yace ko kusa bayya da niyyar yiwa kowa karya.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG