Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Wata Doka Data Hana Zanga-Zanga a Abuja

Migrants carry a raft, after being rescued by the Libyan coastguard, at a naval base near the capital Tripoli, Libya. The bodies of 85 migrants have been found washed up on the coast of Libya, a major departure point for the sea crossing to Europe, the Red Crescent said.

Za'a ci gaba da zanga-zanga a Abuja inji daya daga cikin masu gudanar da zanga-zangar Hadiza Bala

Masu zanga-zanga kan ‘yan mata Chibok da aka sace, gobe zasu ci gaba da zanga-zangar su inji daya daga cikin masu gudanar da zanga-zangar Hadiza Bala Usman,kamar yanda wakiliyar mu Madina Dauda ta bada rahoto.

Wannan ya biyo bayan jawabin da hukumomin ‘yan sandan Najeriya, a Abuja suka yi cewar babu wata doka data hana jama’a yin zanga-zangar lumana da hukumar ‘yan sandan Najeriya ta fitar.

Mai Magana da yawun ‘yan sanda Frank Mba, ne ya furta haka a lokacin da yakewa 'yan jaridu bayani a Abuja.

Wakiliyar mu Madina Dauda, tace wannan na nuni da cewa mai Magana da yawun ‘yan sanda da shi kwamishina ‘yansandan Abuja basu aiki tare kennan,domin jawabansu ya sha banban.

Tunda aka fara zanga-zanga akan ;yan matan chibok fiye da wata daya masu yin wannan zanga-zanga basu tsangwami kowa ba.
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:22 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG