Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'a Nada Damar Yin Zanga-Zanga a Abuja


M.D Abubakar, Sefeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya
M.D Abubakar, Sefeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya

Ana iya yin zanga-zanga kan ‘yan makaratar matan Chibok da aka sace.

Sefeto janar na ‘yan sandan Najeriya, M.D Abubakar yace masu yin zanga-zanga kan ‘yan makaratar matan Chibok da aka sace suna da damar yin zanga–zangar su ta lumana ba tare da an tsangwamesu ba.

Wannan furuci ya biyo bayan sanarwar da kwamishina ‘yan sandan Abuja ya bayar cewa ba’a yarda a sake yin wani zanga-zanga dangane da ‘yan mata fiye da dari biyu da aka sace su a makaranta ba.

Tuni masu gudanar da wadannan zanga-zanga suka shigar da kara a babban kotun Abuja suna kalubalantar jawabin kwamishina ‘yan sandan Abuja, inda suke so kotu ta tabbatar masu ko kwamishina, nada hurumin hanna su a bisa doka.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:53 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG