Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayyanar Hotunan Daliban Da Aka Sace A Kebbi Ya Jefa Iyayensu Cikin Yanayi Na Kaduwa


Wasu daga cikin daliban da suka tsira daga harin 'yan bindigar a jihar Kebbi

A Najeriya daidai lokacin da hotunan yaran nan ‘yan makaranta da yan bindiga suka sace suka karade dandalin sada zumunta na yanar gizo, wasu iyayen yaran sun nuna kaduwa tare da kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi mai yi wa domin samun fitar da yaran.

Masu shiga dandalin sada zumunta na yanar gizo tsakanin jiya zuwa yau sun ci karo da hotonan yaran makarantar Birnin Yauri da ‘yan bindiga suka sace, abin da ya kara tayar da hankalin mahaifan yaran da ma wasu jama'a.

Akan hakan ne wasu iyayen suka yi kira da babbar murya ga gwamnatin Najeriya, da cewa yau kwanan su hudu a Yauri sun zura ido don su ga abinda zai faru da yaransu.

"Muna so mu yi kira ga gwamnati, don Allah su jikanmu su taimake mu, yaran nan suna cikin mawuyacin hali, ina da yara uku a wurin, biyu mata naminji guda. Su hudu ne, amma daya Allah ya yi mata cikawa." In ji daya daga cikin iyayen wadanda suka nemi a sakaya sunayensu.

"Don Allah a taimaka a amso mana yaranmu." Ya kara da cewa.

Daya daga cikin iyayen a nasa bangaren ya nemi ne a bi irin hanyoyin da aka bi a baya, wajen karbo yaran da aka sace.

"Hanyar da aka bi aka karbo yaran Katsina, da kuma hanyar da aka bi aka karbo yaran Kagara, to wannan hanya muke so abi a karbo mana yara, yarona daya ne sai dan abokina." In ji wani daga cikin iyayen.

A makon da ya gabata 'yan bindigar suka far wa makarantar ta Yauri suka kwashe daliban da malamansu.

Hukumomin tsaro sun ce an kubutar da wasu daga cikin daliban da malamansu yayin da rahotannin ke cewa an kashe daya daga cikin daliban.

Yanzu dai jama'a sun zura ido su ga abinda zai faru da yake an shiga rana ta hudu da faruwar lamarin.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

XS
SM
MD
LG