Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BURUNDI: Kungiyar Tarayyar Afirka ta Yi Gargadi Akan Rikicin Kasar


Shugaban Burundi Nkurunzizi

Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU, ta yi gargadin cewa rikicin siyasar Burundi ka iya yin mummunan tasiri akan kasar da kuma kasashen da ke yankin.

Wannan sanarawa da shugabar kungiyar ta AU, Nkosazana Dlimi-Zuma, ta fitar, na zuwa ne kwana guda bayan da aka kashe tsohon shugaban rundunuar sojin kasar, Jean Bikomagu.

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka, suka kashe Bikomagu a kofar gidansa da ke Bujumbura, babban birnin kasar.

Wannan kisa ta biyo bayan wadda akawa mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkar tsaro, Adolphe Nshimirimana a kwananan nan.

“Wannan aika-aika, da sauran munanan tarzoma da aka gani a ‘yan watannin nan, na nuni da irin girman matsalar da kasar ta Burundi ke fuskanta, ana kuma iya samun yiwuwar karin tashin hankali a kasar da ma sauran kasashen da ke yankin.” In ji Dlamini-Zuma.

Ta kuma kara jaddada bukatar yin zaman sulhu domin samar da maslaha ga rikicin kasar.

Burundi ta tsunduma cikin rikici ne tun bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya ayyana shirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na uku, matakin da ‘yan adawa suka kalubalanta.

A watan Yuli aka sake zaben shugaba Nkrunziza, zaben da ake ta ikrarin yana tattare da kurakurai.

XS
SM
MD
LG