Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BURUNDI: Amurka Zata Dakatar da Tallafin da Ta Ke Ba Kasar


Masu zanga zanga a Burundi

Amurka tace zata dakatar da wasu shirye-shiryen bada tallafi da take baiwa kasar Burundi, saboda cin zarafin da ‘yan sandan kasar sukayi wa masu zanga zanga

Jama'a sun fito yin zanga zanga ne domin nuna rashin amincewar su da aniyar shugaban kasar na fitowa tsayawa takara a karo na uku.Haka kuma Amurka ta ce akwai kurakurai a cikin zaben ‘yan majalisun da akayi.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar a jiya Alhamis tace, shawarar da Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya yanke na fitowa takara karo na uku, ta yi sanadiyar mutawar mutane dayawa, da tilastawa ‘yan kasar Burundi sama da dubu 144 gudu zuwa kasashen makwabta, harma da janyo tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Gwamnatin ta Amurka tace shawarar gwamnatin Burundi na cigaba da zaben ‘yan majalisun da akayi 29 ga watan Yuni, duk kuwa da cewa babu wani zaman lafiyar da za’a iya gudanar da zaben, ya kara dagula lamarin. Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bukaci gwamnatin ta Burundi da ta saurari kiranye-kiranyen da kasashe ke yi mata na ta dakatar da zaben shugaban kasar da aka shirya yi 15 ga wannan watan.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG