Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Canada Na Shirin Baiwa Meng Beli


Meng Wanzhou

Kotu a Canada na duba yiwuwar ko zata baiwa shugabar katafaren kamfanin fasahar nan na Huawei beli, ya yin da take jiran ganin ko za a mika ta Amurka domin a tuhumeta a can.

Jiya Litinin kotun dake birnin Vancouver ta ci gaba da sauraron shaidu kan belin Meng Wanzhou.

Lauyoyin Meng, sun nemi kotu da ta baiwa wadda suke karewa beli, suna mai cewa idan aka yi la’akari da kamfanin fasahar da kuma kudin beli na miliyoyin daloli zasu tabbatar da ganin bata gudu ba. Suka kuma ce idan Meng ta gudu daga kasar, hakan zai zamanto abin kunya ga kasar China, ya kara da cewa wannan ma ba zabi bane gareta.

Su kuma lauyoyin gwamnati masu shigar da kara sun bayyana cewa bai kamata a baiwa Meng beli ba, dalilinsu shine tana da hanyoyi da kuma babban dalilin da zai sa ta gudu.

Jiya Litinin jaridar kasar China ta Global Times ta kira matakin da Canada ta dauka akan Meng da cewa rashin Imani ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG