Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Dangari: Tarihin Garin Kwarau a Jihar Kaduna


Wurin dibar ruwa a garin Bandiagara dake Mali
Wurin dibar ruwa a garin Bandiagara dake Mali

Shirin Da Dangari na wannan makon ya leka gidan rediyon Nagarta da ke Kaduna don lalubo mana tarihin garin Kwarau da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna da ke Najeriya. Nasiru Yakubu Birnin Yero ya yi hira da basaraken garin.

WASHINGTON, DC - Mai Unguwa Musa Dahiru Wakili Sarkin Kwarau, ya fadi cewa mutane uku ne suka kafa garin Kwarau, wato Isau, Maisaje da Hana aiki.

Tarihi ya nuna cewa garin Kwarau ya yi suna wajen ginin tukunya da noma wadda ya yi tasiri sosai a garin musamman noman rake, doya da rogo.

A ta fannin kasuwanci kuma, a baya hada-hadar kasuwanci ta linka har kusan sau goma idan aka kwatanta da yanzu saboda yadda kasuwar ta yi suna. Mai unguwa ya koka da cewa ba su da madatsar ruwa da al'umar yankin zasu iya yin noman rani.

Saurari cikakken shirin cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:59 0:00

XS
SM
MD
LG