Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Fannonin Kiwon Lafiya Na Samun Horon Kwarewa


Likitoci
Likitoci

Kimanin dalibai 50 ne da suka yi nazari a fannonin kiwon lafiya daban daban a jami’o’in kasashen waje ke samun horon kwarewa dana sanin makamar aiki a asibitin koyarwa na Aminu Kano a Najeriya.

Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da fuskantar karancin jami’an kiwon lafiya a asibitoci da cibiyoyin kula da kiwon lafiyar jama’a a sassan kasar.

Dailiban wadanda suka yi karatu a jami’o’in kasashen nahiyar Asiya da Turai da kuma Afrika, kamar Burtaniya da Turkiyya da China da Misra da Sudan da Malasiya da Indiya da kuma Uganda na samun horo karkashin kulawar manya kuma kwararrun likitoci da masana kimiyyar fasahar harhada magunguna kana da farfesoshi a sauran fannonin kiwon lafiyar bil’adama.

Farfesa AbdulRahman Abba Shehe dake zaman mataimakin shugaban asibitin koyarwa na Aminu Kano ya yi karin haske game da yanayin daliban dake karbar horon wadda asibitin ya kwashe shekaru biyar yana bayarwa ga daliban dake nazarin kiwon lafiya a kwalejojin nazarin kiwon lafiyar jama’a da jami’o’I a cikin da wajen Najeriya.

Wasu daga cikin daliban sun yi tsokaci dangane da yanayin tsarin sanain makamar aiki da bada horo a asibitin koyarwar na Aminu Kano.

Sai dai farfesa AbdulRahman Abba yace koda yake akwai wasu rukunin daliban da ba asalin ‘yan Najeriya ba ne, amma yanayin horon da suke samu na bai daya ne, inda ake cakuda su da daliban Jami’ar Bayero wadanda mallakar asibitin ne.

Duk da wannan ci gaba, har yanzu mazauna karkara na ci gaba da fuskantar barazanar karancin ma’aikatan kiwon lafiya, la’akari da yadda galibin likitoci da ma’aikatan jiyya ke kyamar aiki a asibitoci da cibiyoyin kula da lafiyar al’uma na yankunan karkara a Najeriya.

Daga Kano ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:15 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG