Accessibility links

Daruruwan mutane ke neman mafaka a wurare da dama

Yanzu haka dai daruruwan mutane ne ka neman mafaka a wurare daban-daban bayan da suka tsere daga garuruwan Gulak da Minchika, a jihar Adamawa, yayin da ‘yan Boko Haram, suka fatattaki sojoji.

Bayanai dai na nuna cewa hakan ya faru ne bayan da sojoji suka yi yunkurin kwace garin daga hannun masu tada kayar bayan, lamarin da ya ci tura.

Wadanda suka samu tserewa sun ce lamarin yasa daruruwan mutane tserewa domin neman mafaka akan tsaunuka.

Kawo yanzu hukumomin tsaro a jihar ba suce komai ba, yayin da hedkwatan, tsaro ta Najeriya, tace hare-haren ‘yan Boko Haram, na barazana ga ‘yanci da hadin kan kasar.

Amma tace ta dukufa ganin cewa tayi galaba, akan ‘yan ta’adda, da kuma kare martaba da kuma iyakokin kasar.

XS
SM
MD
LG