Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ECOWAS Na Shirin Gudanar Da Babban Taron Gaggawa Game Da Juyin Mulkin Guinea


ECOWAS

Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) na shirin gudanar da wani babban taron gaggawa na musamman kan kasar Guinea da za a fara ranar 9 ga watan Satumba a Accra babban birnin kasar Ghana.

Hakan ya biyo bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban Alpha Conde da wani bangare na sojojin karkashin jagorancin Kanar Mahamady Doumbouya su ka yi.

Yankin a baya ya shirya yin taro kan wata majalisa ta musamman kan sake fasalin hukumomi, amma ya canza ajandar bayan juyin mulkin da aka yi a Guinea.

Duka ECOWAS da Tarayyar Afirka (AU) sun yi Allah wadai da juyin mulkin.

Paul Ijeme masanin harkokin kasa da kasa ne kuma tsohon jami'in ECOWAS. Ya gaya wa wakilin Muryar Amurka Peter Clottey cewa dole ne AU da ECOWAS su kasance da niyyar siyasa don tabbatar da cewa gwamnatocin Afirka suna da hakki kuma su cimma burin mutanen su.

Wannan, a zaman wani ɓangare ne na ƙoƙarin hana hambararwa daga hanun sojoji nan gaba da zaɓen gwamnatocin farar hula da tsarin mulki ya zaɓa.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG