Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gina Birnin Karni A Abuja


Bukukuwan Ranar Samun 'Yancin Najeriya.
Bukukuwan Ranar Samun 'Yancin Najeriya.

Daya ga watan Janairun badi Najeriya zata cika shekaru dari da turawan mulkin mallaka suka hada kudanci da arewacin kasar ta zama kasa daya da yanzu ake kira Najeriya

A shirinta na tunawa da shekara da aka kafata da aka sani Najeriya gwamnatin kasar na shirin gina katafaren birni da zai ci makudan kudi.

A jawabinsa na tunawa da samun 'yancin kasar shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce kasar zata cika shekaru dari da kafata daya ga watan Janairun shekarar 2014. A shekarar 1914 ce gwamnatin mulkin mallaka ta Biritaniya ta hade kudanci da arewacin kasar suka zama kasa daya. Sun yi hakan ne domin saukin mulki ba tare da la'akari da ban-bancen al'adu, kabila ko addini ba.

Bayan jawabin shugaban ne bayyanai suka fito cewa gwamnati na shirin kafa wani makeken birni a Abuja wanda zai ci zunzurutun kudi domin tunawa da karnin. An kiyasta cewa birnin zai ci kudi nera biliyan dubu uku da miliyan dubu biyu ko tiriliyon uku da digo biyu. Wannan na cikin rahoton da tsohon shugaban soji na kasar Janar Abdulsalami Abubakar ya mika wa shugaban kasar shirin gina birnin. Nan take ya ce samun wani birnin da zai kere zamanancin Abuja ya tabbata. Janar Abubakar wanda shi ne shugaban daraktocin da zasu kula da gina birnin ya ce kamfanoni da 'yan kasuwa su ne zasu dauki nauyin gina birnin amma ya bukaci gwamnati da ta tanadi fili da janye haraji kan kayan ginin da za'a shigo dasu daga kasashen waje.

Bayyanai sun nuna cewa gidajen da za'a sayar guda dubu daya da dari biyar ne da zasu mallaki duk abubuwan more rayuwa da ma kyautatacen tsarin tsaftace muhalli. A zahiri dai muhalli nada dan karen tsada a Abuja wanda ke nunawa cewa tun da 'yan kasuwa ne zasu jagoranci aikin ba zasu yiwa masu kananan karfi alfanu ba.

Tsohon ministan Abuja kuma dan kungiyar magina Bala Kaoje ya bada bahasin bukataun gidaje a Najeriya. Ya ce a Najeriya yanzu akwai mutane dake bukatan gida fiye da miliyan goma sha bakwai. Daga cikinsu bincike ya nuna cewa yawancinsu kananan ma'aikata ne dake bukatar tallafi kafin su iya samun muhalli na kansu.

Nasiru Adamu El-Hikaya nada rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG