Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Israila Zata Killace Yankunan Larabawa dake Birnin Kudus


'Yansandan Israila suna duba takardun wata Bafalasdiniya a birnin Kudus
'Yansandan Israila suna duba takardun wata Bafalasdiniya a birnin Kudus

Israila ta dauki matakan dakile hare haren da Falasdinawa ke kaiwa kan yahudawa da suka hada da killace yankunan Larabawa a birinin Kudus.

A Gabas ta Tsakiya, Isra'ila ta baiwa rundunar 'Yansandan kasar izinin killace abunda ta kira "cibiyoyin da suke janyo rikici da zuga a birnin Kudus". Galibin hare haren da aka kai a yankin sun auku ne a yankunan da Larabawa suke a birnin na Kudus.

A cikin sanarwar da ofishin Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayar da safiyar Laraban nan, yace za'a soke takardun izinin zama na din din din na mutane da suka kasance 'yan ta'adda, kazalika wadanda suka kai hare hare za'a a kwace muhallansu.

Birnin na Kudus ya fuskanci wuni mafi muni a ci gaba da hare hare jiya Talata da Falasdinawa suke kaiwa. A cikin wannan wata an kashe akalla yahudawa uku.

Sakataren harkokin wajen Amurka John kerry yace zaiyi balaguro zuwa Isrs'ila da yankin Falasdinu, da zummar tarfa ruwa kan rikicin. Sakataren yayi magana ne a maraicen Talata agogon Washington a sashen koyarda dabarun mulki na jami'ar Harvard.

XS
SM
MD
LG