Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Bauchi Za Ta Taimakawa Makiyaya


Wasu makiyaya suna rawa Bidda Jihar Neja.

Gwamnan jihar Bauchi ya baiwa Fulanin Makiyaya tabbacin walwala da taimaka musu a jihar.

Gwamnatin jihar Bauchi ta bada tabbacin taimakawa al’ummar Fulani dukkan abubuwan da suke bukata domin gudanar da rayuwarsu kamar kowanne dan kasa batare da an musguna musuba. Gwamnan Bauchi Abdullahi Muhammed Abubakar ya shaida hakkan a wani gagarumin taro na kungiyar Fulani Kautal hore a Bauchi.

A cewar gwamnan kungiyar gwamnoni na kokarin shawo kan matsalar kafa dokar hana kiwo da wasu jihohin Arewaci suka kafa. Haka kuma ya jaddada cewa babu wani bafulatanin da za a musgunawa a jihar Bauchi.

Shugaban kungiyar makiyaya ta Kautal Hore, Alhaji Bello Abdullahi, ya yabawa gwamnatin jihar Bauchi kan karamcin da take yiwa makiyaya, haka kuma ya bayyana aniyarsu ta fara zuwa kotu domin kalubalantar masu bata musu suna.

Gwamnatin Najeriya ta dukufa wajen neman hanyar magance matsalar rikicin da ake samu tsakanin fulani makiyaya da manoma, inda a taron kolin ‘kasa da shugaban kasa Mohammadu Buhari ya jagoranta na wannan makon ya mayar da hankali kan batun.

An kwashe lokaci mai tsawo ana tattauna hanyoyin shawo kan matsalar da ta addabi fadin kasar.

An sami asarar rayuka masu yawa tun lokacin da wasu jihohi suka kafa dokar hana kiwo a fili.

Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Mohammed.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG