Accessibility links

Iran Na Kara Shan Matsin Lamba A Hannun Amurka


Donald Trump

Jiya Litinin Shugaban Amurka Donald Trump ya kakaba ma kasar Iran abin da ya kira takunkumi mai zafin gaske na tattalin arziki, wanda takamaimai ya fi shafar shugaban addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Trump ya rattaba hannu kan umurninsa na shugaban kasa wanda ya ce zai hana Khamenei da Iran harkar cinikayya da duniya. Sakataren baitilmalin Amurka Steve Mnuchin ya ce wannan mataki ne da zai tsaida kaddarorin biliyoyin daloli na Iran.

Trump, ya kira wannan umurnin na shi "mai karfi kuma wanda ya dace" a matsayin martanin Amurka ga kakkabo jirgi marar matuki na Amurka da Iran ta yi a makon jiya. Amurka ta ce jirgin na tafiya ne a yankin sararin sama na kasa da kasa, daura da Hormuz, amma ita Iran ta ce jirgin ya shiga yankin sararin samanta.

Saura 'yan mintoci kawai jiragen Amurka su yi barin wuta kan Iran ranar Alhamis, sai Shugaba Trump ya yanke shawarar cewa ba zai dau irin wannan matakin sojin ba saboda harbo jirgin Amurka mara matuki da Iran ta yi, bayan da aka gaya masa cewa harin na iya sanadin mutuwar Iraniyawa kimanin 150.

Yayin da yake jawabin sanarda wannan takunkumin, Trump ya ce, "Ina ganin mun nuna matukar hakuri, amma ba lallai bane mu kara daurewa irin haka a gaba. Amma za mu gwada yanzu."

Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG