Accessibility links

Israila da Falasdinu Na Kokarin Farfado da Shawarwari


Shugaban Amurka Barack Obama da Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da Firayim Ministan Isira'ila Benjamin Netanyahu.

Masu ba Israila da Falasdinu shawarwari suna kokarin farfado da komawa kan teburin shawarar neman zaman lafiya tsakaninsu.

Jiya Litinin mashawartan Isira'ila dana Palasdinawa suka gana a yayinda suke kokarin farfado da shawarwarin samun zaman lafiya tsakaninsu dake digirgire.

Amirka wadda take kokari siga tsakani a rikicin gabas ta tsakiya na shekara da shekaru tace bangarorin biyu sunyi shawarwari masu ma'ana a ranar Lahadi kuma dukkan bangarorin sun bukaci jami'an Amirka da su shirya wani taron.

Amirka tace bangarorin biyu suna kokarin magance rikicin da aka samu a cikin tattaunawar.

Yunkurin da Amirka tayi na fadada lokacin yin shawarwarin zuwa wa'adi na da aka gitta na karshen wannan wata na Afrilu ya cije a makon jiya, bayan da Isira'ila ta canja ra'ayi akan shirin sako Fursunonin Palasdinawa, su kuma Palasdinawa suka farfado da begensu na samun amincewa Majalisar Dinkin Duniya na kasar su ta Palasdinu da ake cacar baki akai.

A yayinda shawarwarin suka cije, sakataren harkokin wajen Amirka ya baiyanawa bangarorin takaicin Amirka, yana mai fadin cewa Amirka zata sake nazarin matsayinta na mai shiga tsakani.
XS
SM
MD
LG