Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Italiya Ta Yi Barazanar Ficewa Daga Asusun Kungiyar Tarayyar Turai


Bakin Haure

Gwamnatin Italiya ta yi kashedi a jiya Juma'a cewa zata ficewa daga gidauniyar Kungiyar Tarayyara Turai, har sai an kwashe wasu mutane 150 da suka makale a cikin wani ruwan jami’an tsaron gabar tekun kasar, lamarin da ya sake kunno da sabon rikicin bakin haure a Turai.

Mutane da dama sun makale a tashar jirgin ruwa ta Sicilian dake Catania a cikin jirgin ruwan Diciotti, tun cikin daren Litinin, saboda gwamnatin Italiya taki yarda a saukesu, har sai kasashe mambobin Kugniyar Tarayyar Turan sun amince su karbi wasu a cikin mutanen.

Luigi Di Maio shine Mataimakin Frai Ministan Italiya yace shi da sauran jami’iyyun siyasar kasar ba zasu yarda su bada euro biliyon 20 ga Kungiyar Tarayyar Turai a duk shekara. Yace zasu rike wani bangare na kudin, har sai an tabbatar da wani kasafi da zai sa ido a kan biliyon 20 na Tarayyar Turan.

Nan da nan helkwatan Kungiyar tarayyar Turai dake Brussel ta maida martani a kan kalaman Di Maio, ta bakin mai Magana da yawun hukumar zantarwar Kungiyar Alexander Winterstein,

Yace kada fa wannan magana ta kaimu ga dorawa juna laifi. Kuma mun amince kalamai marasa kyau da barazana ba zasu kai mu ga warware matsala ba. Kungiyar Tarayyar Turai kungiya ce mai dokoki kuma tana gudanar da ayyukanta a kan dokokinta amma ba barazana ba. Don haka zamu nemi kowane bangare ya hada hannu wurin shawo kan wannan matsala domin taimakawa wadannan mutane kai hade.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG