Accessibility links

Jirgin sama yayi saukar farko a sabon filin jiragen saman jigilar amfanin gona da sauran kayan kasuwanci a birnin Dutsen Jahar Jigawa

Jirgin sama yayi saukar farko a sabon fiilin jirgin saman birnin Dutse, fadar jahar Jigawa kamar yadda kakakin gwamnan jahar Umar Kiari ya shaidawa wakilin Sashen Hausa Ladan Ibrahim Ayawa. Kakakin ya ce jirgin saman mai daukan 'yan mutane kalilan yayi saukar farko a Dutse da misalin karfe goma sha biyu da rabi na rana a karshen mako. Haka kuma jirgin saman ya dauki gwamnan jahar Sule Lamido tare da wasu mukarraban shi zuwa birnin Kano. Kakakin gwamnan na jahar Jigawa Umar Kiari ya ce ba a kammala filin jirgin saman ba amma an ci karfin aikin, kuma nan da wasu 'yan watanni kamar uku zuwa hudu, shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan zai yi bikin kaddamar da filin jirgin saman.

XS
SM
MD
LG