Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'a Su Daina Daukar Cewa Musibu Da Ke Faruwa Wasu Kasashe Ba Su Shafe Su Ba - Shiekh Karibullah Nasir Kabara


Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara
Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara

Yayin da shugabannin kasashen duniya ke ci gaba da tsokaci akan yakin da kasar Russia ke yi da Ukraine,  Malaman addini sun soma karkata hankulansu akan bukatar jama'a su bada tasu gudunmuwa wajen kawo karshen yakin.

Wannan na zuwa ne lokacin da wasu kasashen duniya ke fama da wasu matsaloli da kan iya yin Illa ga zaman lafiya.

Illolin da yakin Rasha da Ukraine ya kawo ga kasashen duniya, wadanda ke yin mummunan tasiri ga jama'a, na zuwa lokacin da wasu kasashen duniya ke fama da matsaloli musamman na rashin tsaro wadanda ke jefa rayukan jama'a cikin kunci.

To sai dai wasu jama'a na kallon musibu dake faruwa a wasu kasashen duniya a zaman abubuwan da kan iya mamaye duniya baki daya idan ba'a kula yadda ya kamata ba.

Shugaban darikar Kadiriya na Afirka, Shiekh Karibullah Nasir Kabara ya ce jama'a su daina daukar cewa musibu da ke faruwa wasu kasashe ba su shafe su ba.

Ya bayar da misali da cutar korona wadda ta fara daga kasar China amma sannu a hankali sai da ta shafi kasashen duniya, ya ce hakama wannan yaki na Rasha da Ukraine in ba'a kula ba zai yi wa duniya illa don haka akwai bukatar jama'a su dage da addu'a don kawo karshen yakin tun bai illata duniya ba.

Wannan bai rasa nasaba da yadda malamai ke fitowa da wasu hanyoyi na fakarda jama'a akan bukatar wanzar da zaman lafiya mai dorewa kamar yadda ya wanzu a duniya a shekaru da suka gabata, kamar koyi da magabata.

Shiekh Karibullah yace idan a ka yi koyi da koyarwar su Shehu Usmanu Danfodiyo za'a cewa koyarwa ce wadda ta wanzar da zaman lafiya.

Yadda aka samu zaman lafiya bayan kafuwar wasu dauloli a duniya na kasancewa abin koyi ga na baya, kamar yadda shugaban kadiriya na Jamhuriyar Nijar Shiekh Sanda Agadez wanda ya maganta ta bakin limamin masallacin Jumu'a na Tahoua Hamza bin Bello ya ce koyi da koyarwar Daular usmaniya kan iya taimakawa.

Ya ce Shehu Usmanu Danfodiyo ya koyar akan biyar koyarwar fiyayyen halitta domin samun wanzuwar zaman lafiya.

Musulunci da Kiristanci sune ke da yawan mabiya a fadin duniya, kuma duk suna nuni akan bukatar koyi da magabata don samar da zaman lafiya.

Reverend Yakubu Oro, malami ne na mabiya addinin kirista. Ya ce idan aka duba koyarwar Yesu Almasihu za a ga cewa koyarwa ce ta zaman lafiya, kuma idan aka yi amfani da koyarwar za a samu amfani kwarai da gaske, ya ce lokacin da Yesu Almasihu ya rayu cikin duniya har wadanda suka kuntata masa ya kyautata musu abin da ya nuna irin zaman lafiya da ya kamata Masubi su yi koyi.

Daga cikin hanyoyin da ake sanin ayyukan magata akwai shirya wasu taruka, kamar taron tunawa da haihuwar Shehu Usmanu Danfodiyo da kungiyar kadiriya ta gudanar a Sakkwato inda malamai suka yi tsokaci akan ayyukan sa da ya kamata ayi koyi dasu.

Saurare rahoton Muhammad Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

XS
SM
MD
LG