Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Joe Biden Ya Fara Shirye-shiryen Karbar Mulki


Shugaba Joe Biden mai jiran gado da Kamala Harris mataimakiyarsa sun bude wani shafi ta yanar gizo wanda zai maida hankali kan shirye-shiryen karbar mulki.

Joe Biden na Jam’iyyar Democrat, wanda ake gani shi ya samu nasara akan shugaba Donald Trump na jam’iyyar Republican a zaben shugaban kasar Amurka da aka yi mai cike da takadamma, ya fara shirye-shiryen karbar mulki idan aka rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairu, inda ake kuma tunanin zai yi watsi da wasu muhimman tsare-tsare da Trump ya samar.

Hakan na faruwa ne yayin da Trump ya ke kalubalantar sakamakon zaben na ranar 3 ga watan Nuwamba ta hanyar kararrakin da ya shigar, inda ya ke ikirarin cewa an tafka magudi a kidayar wasu jihohi da dama da Biden ya lashe da ‘yar tazara tare da kuru’un wakilan zabe, matakin da ya ke fatan zai sa a karbe nasarar ta Biden a ba shi don ya samu damar yin wa’adinsa na biyu, duk da cewa babu wata hujja da ya gabatar.

Biden da ake gani shi ya lashe zaben da abokiyar takararsa Kamala Harris, wacce ita ce zababbiyar mataimakiyar shugaban kasa, sun bude wani shafin yanar gizo a ranar Lahadi 8 ga watan Nuwamba wanda zai mayar da hankali kan shirye-shiryen karbar mulki, inda suka ce ba tare da bata lokaci ba, za su mayar da hankali kan annobar coronavirus, sauyin yanayi da kuma matsalar wariyar launin fata.

Shi dai Trump ya ki amincewa da shan kaye ya kuma ki kiran Biden.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG