Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kafa Kwamitin Bincike Da El Rufai Ya Yi Abin Dariya Ne – NLC


Shugaban NLC na kasa, Ayuba Wabba
Shugaban NLC na kasa, Ayuba Wabba

Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta mayar da martani ga gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufai kan matakin kafa kwamitin bincike da ya dauka don gano abubuwan da suka faru a gabani da lokacin yajin aikin da kungiyar ta jagoranta a watan Mayu.

NLC ta jagoranci zanga-zanga a tsakanin 16 zuwa 19 ga watan Mayu inda kungiyar ta nemi gwamnatin jihar ta janye matakin korar dubban ma’aikata da ta yi.

Yajin aikin gargadin ya kassara harkokin yau da kullaum a jihar ta Kaduna na tsawon kwana hudu inda aka rufe harkokin sufuri da dauke wutar lantarki.

Gwamna Nasiru El Rufai​ ya zargi NLC da yunkurin kassara tattalin arzikin jihar, inda har ya ayyana shugabanta Ayuba Wabba a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

A ranar Talata, gwamna Nasiru El Rufai​, ya kafa wani kwamiti mai mutum bakwai karkashin jagorancin Justice Ishaq Bello don bincikar irin rawar da NLC da shugabanninta suka taka da sauran hukumomin sufuri, da na samar da wutar lantarki da jami’an tsaro.

Karin bayani akan: Ayuba Wabba, NLC, Nasiru El Rufai​, Ishaq Bello, Kaduna, Nigeria, da Najeriya.

Sai dai a sanarwar da NLC ta fitar dauke da sa hannun Ayuba Wabba, ta kwatanta matakin da gwamnan ya dauka na kafa kwamiti a matsayin abin dariya.

“Ko da yake, muna matukar girmama shugaban kwamitin, Justice Ishaq Bello da sauran mambobin kwamitin, amma da sai mu ce wannan abin dariya ne matuka, kuma wuce makadi da rawa ne a ikon da gwamnan yake da shi, sannan barnata dukiyar jiha ne.” Sanarwar kungiyar ta NLC wacce ta wallafa a shafinta na yanar gizo ta ce.

A cewar sanarwar ta NLC, matakin yajin aikin na gargadi da aka yi, an gudanar da shi ne bisa yadda doka ta tanada karkashin kundin tsarin mulki na 1999 da aka yi wa garanbawul.

“Yana kuma da muhimmanci mu nuna cewa, Mr. El Rufai​ ko gwamnatin jihar Kaduna na cikin wannan rikici. Daya daga cikin ginshikan doka shi ne, babu yadda za ka iya zama alkali a shari’ar da ta shafe ka, saboda haka, ba mu ga yadda El Rufai​/Jihar Kaduna za su iya zama alkalai a wannan batu ba.”

El Rufai​ dai ya ba kwamitin kwana 60 ya kammala aikinsa inda ake sa ran zai gabatar da shawarwari ga gwamnati.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG