Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KANO: Maniyyata Sun Bayyana Alhini Game Da Janye Aikin Hajjin Bana


Alhazai A Saudiyya

Maniyyata aikin hajin bana da masu kamfanonin jigilar alhazai ta jirgin yawo a Najeriya na bayyana alhini dangane da sanarwar hukumomin Saudiyya na janye aikin hajji ga ‘yan kasashen waje. 

Ranar asabar mahukuntan kasa mai tsarki suka fitar da sanarwar cewa, ‘yayan kasar saudiyya da baki mazauna can ne kawai ke da damar gudanar da aikin hajjin bana, amma su ma bisa cika sharrudan kiyaye kamuwa ko yada cutar Corona da aka shimfida.

Kamar sauran kasashe, yanzu haka dai wannan mataki ya dagula lissafin maniyyata daga Najeriya.

Wasu daga cikin dinbin masu aniyar sauke farali a bana daga jihar Kano da Muryar Amurka ta yi hira da su sun nuna bacin ransu game da wannan lamarin saboda sun sa a ran su cewa sun riga sun zama alhazai.

Karin bayani akan: jihar Kano, Muryar Amurka, Corona, Nigeria, da Najeriya.

Su ma masu kamfanonin dake shirya jigilar alhazai zuwa kasa mai tsarki ta jirgin yawo sun koma game da wannan yanayi da aka tsinci kai.

Fiye da alhazai dubu 90 ke sauke farali a kowace shekara daga Najeriya kuma kimanin dubu 7 daga cikin su ‘yan jihar Kano ne.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG