Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kokarin Dinke Sabuwar Baraka Tsakanin 'Yan Jam'iyyar Republican


Fadar shugaban Amurka da shugaban majalissar dattijai sun yi kokari su dinke barakar da ke kara fadada a jam’iyyar Republican mai mulki.

Sabuwar rashin jituwar da ta kunno kai a majalissar ita ce lokacin da sanata Jeff Flake, na jihar Arizona ya caccaki halayyar shugaba Trump, ya kuma sanar da cewa ba zai sake tsayawa takara ba a shekara mai zuwa idan Allah ya kaimu.

Flake, wanda wannan shine karon sa na farko akan wannan mukamin, wanda kuma yayi aiki a majalissar wakilai na tsawon shekaru 12, ya ce “batan basira ne babba a yi shiru yayinda ake ruguza al’adu da muhimman abubuwan da suka hada kan Amurka, yayinda kuma tunanin da ake amfani da harufa 140 wajen rubutasu ke barazana ga kawance da yarjejeniyoyin da ke tabbatar da zaman lafiya a fadin duniya.

Flake ya kara da cewa jam’iyyar Republican ta dade tana yaudarar kanta akan cewa Trump zai yi abinda ya dace.

Da yake maida martani a shafin Tweeter, shugaba Trump yace “sanata Flake da Corker sun gane cewa ba zasu ci zabe ba shi yasa, yanzu suka fusata suke bakaken maganganu

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG