Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatan Kamfanin Man Fetur A Jamhuriyar Nijar Sun Fara Yajin Aiki


Zanga Zangar Ma'aikatan Kamfanin Man Fetur Na CNPC A Nijar

A jamhuriyar Nijar ma’aikatan aikin hakar Man Fetur sun fara yajin aikin kwanaki biyu, domin nuna rashin jin dadin ga yadda shugabannin kamfanin CNPC ke fifita ma’aikata ‘yan kasar China fiye da su ‘yan kasa musamman kan batun shugabanci da albashi.

Yajin aikin ya biyo bayan nasarar da ma’aikatan suka samu a kotu saboda watsin da tayi da wata karar da shugabannin kamfanin CNPC mai ayyukan hakar Man Fetur a kasar Nijar suka shigar, inda suka kalubalantar halaccin kungiyar ma’aikatan.

Fifita ma’aikata ‘yan China akan takwarorinsu na Nijar na daga cikin manyan abubuwan da masu yajin aikin ke zargin shugabannin kamfanin na CNPC da aikatawa. A cewar ma’aikatan babu wani tsarin aiki a kamfanin, domin duk kankantar mukamin ma’aikaci dan kasar China zai iya baiwa kowanne ma’aikacin Nijar umarnin yin aiki, idan kuma mutum bai yi ba to zai rasa aikinsa.

A cewar wani ma’aikaci mai suna Tasi’u Ibrahim, yadda lamarin ya tsananta murabus din shugaban kamfanin ya zama wajibi, kamar yadda doka ayi tanadi.

Bayanai daga rijiyoyin Mai na Agadem na nuni da cewa wannan yajin aiki yayi tasiri sosai akan ayyukan hakar ‘danyan Mai, saboda yadda ma’aikata ‘yan Nijar suka amsa kiran kungiyar Sinatrap wanda yake kusa a kungiyar ma’aikatan Man Fetur.

Muryar Amurka tayi kokarin tuntubar shugabannin kamfanin CNPC ta wayar tarho, domin jin ta bakinsu kan wannan yajin aiki, sai dai jami’in hulda da jama’a na kamfanin yace a bashi dama ya sanar da manyansa.

Takun saka tsakanin ‘yan kasar China dake shugabancin kamfanin CNPC da ma’aikatan Nijar, wani abu ne da ya samo tushensa tun a ranakun farkon soma ayyukan hakkar Man Fetur din Nijar a shekara ta 2012, saboda abin da wasu ke yiwa kallon keta dokokin kasa daga ‘yan kasar China.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG