Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Amurka Zata Binciki Tsohon Shugaban Ma’aikatar Kare Muhalli


Scott Pruitt
Scott Pruitt

Tsohon shugaban ma’aikatar kare muhallin Amurka Scott Pruitt zai fuskanci tambayoyi daga majalisa a yau Alhamis bisa zargin almubazzaranci da saba ka'idar aiki a lokacin da yake bakin aiki.

Pruitt zai bayyana gaban kwamittoci biyu na majalisar wakilai domin yin bayani kan kasafin kudin ma'aikatar, sai dai 'yan majalisar dokoki zasu tambaye shi akan yadda ya kashe kudin kan tafiye tafiyen da yayi a jirgin sama, a kujerun kawa, da jami'an tsaron shi, da kuma dakin da ya kama haya a Washington.

Ofishin kididdigar kudaden gwamnati ya bayyana a farkon watan nan cewa, ma’aikatar ta sabawa doka a lokacin da ta amince da gina daki na zunzurutun kudi har dalar Amurka dubu 43 wanda yake hana fitar sauti domin amfanin Pruitt.

Amman ma’aikatar ta kare hakan, da cewa, ya zama dole a gina shigifar domin kare Pruitt daga barazanar jama’a tare da yin ayyukan sirri.Wadansu ‘yan majalisa ‘yan jam’iyyar Republican sun shiga sahun ‘yan jam’iyyar democrat domin kira ga gwamnati da ta binciki Pruitt.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG