Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Kiyasta Mutane Milyan 68.5 Ke Gudun Hijira


A halin yanzu hukumar dake lura da al’amuran 'yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya ta ce mutane miliyan 68.5 a fadin duniya aka tilasatawa gudu su bar gidajensu a shekarar data gabata saboda yaki, tashin hankali ko aka tsanantawa.

Kwamishinan 'yan gudun hijira na Majalisar dinkin duniya, Filippo Grandi, ya gayawa manema labarai a Geneva, yau Talata cewa yawan ‘yan gudun hijira na shekarar 2017 ya zarce na shekarar 2016 da kusan mutane milyan 3.

Ya ce an samu karin 'yan gudun hijira fiye da mutane miliyan 16 a bara, a dalilin yake-yake da tashe tashen hankulan da suka ki ci suka ki cinyewa ko aka kasa kawo karshen su, kuma hakan ya janyo matsi ga mutane farar hula.

Grandi ya ce fiye da kashi biyu bisa uku na 'yan gudun hijira sun fito ne daga kasashe kalilan da suka hada da Afghanistan, Syria, Sudan ta Kudu, da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG