Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zabe A Ivory Coast Ta Ayyana Shugaban 'Yan Hamayya Ouattara A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Zagaye Na Biyu


Ivorian soldiers stand guard at the entrance to electoral commission headquarters in Abidjan.

Yau Alhamis ce shugaban hukumar zaben ya bayyana cewa madugun 'Yan hamayya Alassane Outtara ne ya lashe zaben da kashi 54 cikin dari na kuri'u da aka kada,yayinda shugaban kasa Laurent Gbagbo ya sami kashi 46

Hukumar zaben kasar Ivory Coast ta sanar da dan takarar shugaban kasar na jam’iyar hamayya Alassane Quattara ya lashe zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka gudanar ranar Lahadi.

Shugaban hukumar zaben ya bayyana yau alhamis cewa, Mr. Quattara ya doke shugaban kasar Lauren Gbagbo inda ya sami kashi 54% na kuri’un yayinda shugaban kasar ya tashi da kashi 46%. An sanar da sakamakon zaben ne bayan sa’oi 16 da cikar wa’adin da aka dibarwa hukumar na sanar da sakamakon zaben wanda ya cika karfe sha biyun daren jiya Laraba.

Poster of Ivory Coast opposition leader Alassane Ouattara, 25 Nov 2010.
Poster of Ivory Coast opposition leader Alassane Ouattara, 25 Nov 2010.

Babu tabbacin ko majalisar kundin tsarin mulkin kasar zata amince da sakamakon zaben, wadda bisa ga dokar kasar, tilas ta tabbatar da sakamakon zaben. Yau alhamis shugaban hukumar Paul Yao D’dre yace hakin hukumar ne sanar da ainihin sakamakon zaben domin hukumar ta gaza sanar da shi cikin lokacin da aka dibar mata. Muna da Karin bayani bayan labarai.

XS
SM
MD
LG