Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Kasashe Sun Yi Kira Ga Gbagbo Da Ya Mutunta Sakamakon Zabe


Alassane Ouattara yana kada kuri'arsa a zagayen farko na zaben shugaban kasa a Abidjan

Shugaban majalisar tsarin mulkin Ivory Coast, na hannun damar shugaba Gbagbo, yace sakamakon da hukumar zabe ta bayyana ba na halal ba ne.

Fadar shugaban Amurka ta White House ta yi kira ga dukkan sassan kasar Ivory Coast, ko Cote D'Ivoire, da su mutunta sakamakon zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar.

Jiya alhamis ne hukumar zabe ta kasar Ivory Coast, ta ayyana shugaban hamayya, Alassane Ouattara, a zaman wanda ya lashe zaben da kashi 54 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da shugaba Laurent Gbagbo ya samu kashi 46 cikin 100.

Amma kuma nan da nan sai Majalisar Tsarin Mulki ta kasar ta ce wannan sakamakon ba na halal ba ne. Shugaban majalisar, wadda ita ce mai tabbatar da sakamakon zabe, ya fito a telebijin yana fadin cewa tun da ba a fadi sakamakon zuwa 12 na daren laraba kamar yadda tsarin mulki ya yi tanadi ba, wannan sakamakon ba na gaskiya ba ne.

Shugaban ita wannan majalisa, Paul Yao N'Dre, na hannun damar shugaba Laurent Gbagbo ne.

Wani kakakin fadar shugaban Amurka ta White House, ya ce tun da 'yan kallo sun bayyana cewa matsalolin da aka fuskanta lokacin zaben ba su isa sauya sakamakon zaben ba, ya zamo wajibi ga dukkan sassan da su yi na'am da shi.

Haka kuma a jiya alhamisar, shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa da Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira ga majalisar tsarin mulkin ta Ivory Coast da ta mutunta zaben da jama'a suka yi. Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya yayi kashedin cewa zai dauki matakin da ya dace a kan duk wani wanda ya nemi tauye tsarin zabe na kasar.

Jim kadan a bayan da aka fadi sakamakon zaben, sojojin Ivory Coast sun fito a telebijin su na fadin cewa sun rufe dukkan iyakokin kasar ta kasa ta ruwa da kuma ta sama, yayin da majalisar yada labarai ta dakatar da watsa labarai na dukkan kafofin yada labaran kasashen waje a kasar.

Wadannan kafofi su ne suka yada sanarwar da hukumar zabe ta bayar cewa Ouattara ya lashe zaben. Gidan telebijin na kasar ya ki yarda ya bayyana sakamakon.

XS
SM
MD
LG