Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Tsarin Mulki a Ivory Coast Ta Rusa Zaben Shugaban Kasar Da Hukumar abe Tace Shugaban 'Yan Hamayya Alassane Outtara ne Ya lashe


A young man throws a tire onto a fire during a protest by supporters of opposition leader Alassane Ouattara in Abidjan, 03 Dec 2010.

Kotun tsarin Mulkin kasar ta kuma ayyana Shugaba laurent Gbagbo a matsayin wanda ya lashe zaben .

Kotun Tsarin mulki a Ivory Coast ta rusa sakamakon zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka yi ranar lahadi da ta shige.Daga nan kotun ta ayyana shugaba Laurent Gbagbo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Yau jumma’a ce kotun ta tsaida shawarar rusa sakamakon zaben da hukumar zaben kasar ta bayyana jiya Alhamis,da ta ayyana shugaban ‘yan hamayya Alassane Ouattara,wanda ya sami nasara. Shugaban majalisar Paul Yao N’Dre,yace majalisar ta rusa sakamakon zaben daga yankuna bakwai na arewacin kasar, saboda bincike da ta gudanar ya nuna an tafka magudi.

Poster of Ivory Coast opposition leader Alassane Ouattara.
Poster of Ivory Coast opposition leader Alassane Ouattara.

Galibin goyon bayan da Mr. Ouattara yake da shi daga arewacin kasar ne. Magoya bayan Mr. Ouattara sun fantsama kan titunan birnin Abidjan,jim kadan bayan kotun ta bayyana shawara da ta yanke,suna jifa da duwatsu, da tada wuta. Akwai ‘yansdan kwantar da tarozma a wurin,amma basu sabaki ba. N’Dre yace a sabuwar kididdiga ta tayi,shuga Gbagbo yana da kashi 51 cikin dari,yayinda Mr. Ouattara kuma yake da kashi49 cikin dari.

Shi Mr. N’Dre na hanun daman shugaba Laurent Gbagbo ne. Ahalin yanzu kuma, wakilin MDD na musamman a Ivory Coast Y.J. Choi bai amince d a shawarar kotun tsarin mulkin na bai wa shugaba Laurent Gbagbo nasara ba. Mr. Choi yace yana goyon bayan sakamamonda ya nuna Mr. Ouattara ne ya lashe zaben.

XS
SM
MD
LG