Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Kidaya Kuri'u Na Zaben Fitar Da Gwani Na Shugaban Kasa A Ivory Coast


Masu jefa kuri'ar da suka fusata ganin an kasa bude rumfar zabe kan lokaci, sun karya kofar wurin zabe a wata unguwa mai suna Abobo a birnin Abidjan, lahadi 28 Nuwamba, 2010.

Bangaren shugaba Laurent Gbagbo da na mai hamayya da shi Alassane Ouattara duk su na zargin an aikata magudi a zaben

An fara kidaya kuri'u a kasar Ivory Coast ko Cote D'Ivoire, a bayan zaben fitar da gwani na shugaban kasa da ya haddasa zub da jini kafin ranar zabe, da kuma zarge-zargen cin zarafi ranar zaben daga dukkan sassan biyu.

Wani kakakin shugaba Laurent Gbagbo yace ba a gudanar da zaben tsakani da Allah ba a yankunan arewacin kasar inda abokin hamayyarsa Alassane Ouattara yake da karfi da goyon baya.

Shi kuma manajan kyamfe na Mr. Ouattara, Marcel Tanon, yayi zargin cewa masu jefa kuri'a da yawa sun kasa isa rumfunan zabe jiya lahadi a saoda yadda magoya bayan shugaba Gbagbo suka rika tare su, su na hana su kaiwa ga wuraren jefa kuri'un nasu.

Shugaban tawagar 'yan kallo ta Tarayyar Turai, Cristian Preda, ya ce lallai an ga shingaye a wurare da dama inda ake hana magoya bayan Mr. Ouattara da na Mr. gbagbo kaiwa ga rumfunan zabe.

Miliyoyin 'yan kasar ta Cote D'Ivoire sun kada kuri'unsu jiya lahadi a wannan zaben da aka shirya domin sake hade kasar wadda yakin basasa na 2002 ya raba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG