Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisun Amurka Sun Sabawa Trump A Kan Batun Kashe Kashoggi


Zauren Majalisar Amurka
Zauren Majalisar Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yace yana sane da matsaya mai tsauri da ‘yan majalisun tarayyar Amurka suka dauka a kan dadaddiyar kawayensu Saudi Arabia, lamarin da ya kwatanta da abin tarihi.

A shekaranjiya Alhamis ne majalisar dattawan Amurka ta rattaba hannu a kan kudirin kawo karshen gudunmuwar da Amurka ke yiwa rudunar hadin gwiwa da Saudiya ke jagoranta a yakin Yamal, a wani matakin yin Allah wadai da kashe dan jaridar Saudiyar nan.

Mun ga kuri’ar da aka kada a shekaranjiya. A koda yaushe muna mutunta hukuncin da bangaren majalisa ya zartar, inji Pompeo yana fadawa manema labarai a jiya Juma’a a nan Washington. Yace sau tari muna tuntubar majalisun kasar domin mu fahimci damuwarsu kuma mu yi iya kokarinmu mu yi musu bayani a kan manufofin mu.

A wata ganawa da manema labarai tare da sakataren tsaro Jim Mattis da ma takwarorin aikinsu na Canada, Pompeo ya kara da cewa shugaba Donald Trump ya himmantu wurin kare Amurka, yayin da kuma yake kokarin ganin an hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki na kashe Jamal Kashoggi.

Bayan tabka mahawara na sa’o’I da dama a ranar Alhamis, majalisar dattawa da Republican ke da rinjayi ta kada kuri’a 56 na masu neman yanke gudnmuwa ga Saudi Arabia a yakin Yamal kana kuri’u 41 na wadanda basu ra’ayin yankewa. Daga bisani majalisar ta tabbatar da daftari na biyu da kuri’ar jin murya. Matakai biyu da majalisar ta dauka duk sun sabawa matsayar gwamnatin Trump wacce ta sha bayyana musunta a kan wannan batu da ka iya kawowa huldan Washington da Riyadh tsaiko.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG