Accessibility links

'Yan Najeriya Sun Soma Tofa Albarkacin Bakinsu Kan Ministocin da Shugaban Kasa Ya Kora


Shugaba Goodluck Jonathan

Ba zato ba tsammani sai gashi gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta yi watsi waje da ministoci hudu har da wadda ake ikirarin shafaffa ce da mai

Kodayake gwamnatin tarayyar Najeriya tace ministocin da suka fice murabus suka yi amma wasu na ganin lamarin daban musamman dangane da ita ministar dake kula da harkokin jiragen sama Stella Oduah wadda majalisar wakilai da kungiyoyi dake yaki da cin hanci da rashawa suka bukaci a koreta domin abun kunyan nan da ta yi.

Stella Oduah wadda har zanga-zanga kungiyoyi suka yi domin a koreta an kalubaleta kan digiri na biyu da tace ta samu daga wata jami'a a Amurka. Alhaji Alhasan Abubakar dan kasuwa dake zaune a Abuja yace shugaban kasa ya kyauta da ya koresu domin akwai korafe-korafe a kansu. Ya kara da cewa "Dama can ba bukatun shugaban kasa suka sa a gaba ba bukatun kansu ne"

Sai dai an ce watakila an sallami ministan Neja Delta domin ya shiga takarar gwamna a jiharsa haka ma Olubolade ministan 'yan sanda. Shi ma Dr Yarima Ngama ya dade yana neman kujerar gwamnan Yobe. Ga ma abun da yake cewa. "Kowa ya san jihar Gombe ANPP ke mulki bata yi masu komi ba suka jire suka kawo PDP aka cigaba. Isha Allah mutanen Yobe zasu kawo PDP acigaba". Yace dole ya ba gwamna Ibrahim Geidam tsoro domin a matsayinsa na karamin minista ya kai ayyukan cigaba a Yobe har guda ashirin. Dr. Ngama yace PDP ce kadai zata warkar da ciwon kan Yobe ba APC ba.

Shugaban matasan PDP na jihar Yobe Ado Adamu Bomboi yace su suka bukaci ministan ya dawo gida yayi takara. Yace "in dai siyasa za'a yita don mutunci ko kuma don abun da za'a bada ko kuma don maganar da za'a yi ko kuma don abun da kayi...to Dr Yarima za'a kawoshi a gwamnati a Yobe za'a rantsar da shi mu yi masa handoba ya cigaba da taimakon talaka..." Ya kara da cewa abu biyu ne mutun zai rike a rayuwarsa, daga Allah sai talaka. In ji shi "in ka rike wadannan guda biyu baka da yunwa baka da hawan jini baka da rashin lafiya har iyakan ranka" Yace shi ya ga wasikar yin murabus din nasa kana yace masa ya je ya bar aiki su dawo su yi siyasa.

XS
SM
MD
LG