Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Kada Kuri'a a Catalonia Sun Yi Kememe Sun Fita Cibiyoyin Zabe


Wani dna sanda yana kallon wani mai kada kuri'a a zaben raba gardama na yankin Catalonia mai so ya balle daga kasar Spain, ranar 29 ga watan Satumba 2017.
Wani dna sanda yana kallon wani mai kada kuri'a a zaben raba gardama na yankin Catalonia mai so ya balle daga kasar Spain, ranar 29 ga watan Satumba 2017.

A Spain ko kuma Andalus, masu zanga zanga sun yi cunkoso a Barcelona domin nuna adawarsu da shirin zaben raba gardama kan ballewar yankin Catalonia daga kasar ko kuma akasin haka yayin da ake shirin kada kuri'ar a yau Lahadi.

Masu kada kuri’ar raba gardama a yankin Catalonia sun yi sammako a yau Lahadi zuwa cibiyoyin kada kuri’a domin yin zaben da hukumomin Spain suka haramta.

Kotun kundin tsarin mulkin kasar ta ba da umurnin jingine zaben, lamarin da ya sa gwamnatin tarayya ta Andalus ta ayyana shi a matsayin haramtacce.

Hukumomin Spain sun ce sun rufe cibiyoyin zabe da dama sannan sun karbe kuri’un, sai dai duk da haka hukumomin yankin na Catalonia sun yi gaban kansu wajen gudanar da zaben, inda suka dasa akwatunan zaben a wasu cibiyoyi.

Daruruwan mutane wadanda suke goyon bayan zaben ne dai suka kafa sansanonin wucin gadi a makarantu da sauran wuraren zabe domin a tabbatar sun kasance a bude ga masu zabe a yau Lahadi.

Wani babban jami’an tsaron kasar ya ce sun yi nasarar rufe akalla rumfunan zaben sama da dubu-biyu-da-dari-uku, da aka tanadar.

Ya kuma kara da cewa hukumomin kasar ta Spain sun yi nasarar kwance wata fasahar zamani da za a yi amfani da ita, wajen kidayar kuri’u, matakin da ya ce zai tilasta dakatar da zaben na raba gardamar ballewar yankin na Catalonia daga Spain.

zaben sama da dubu-biyu-da-dari-uku, da aka tanada domin gudanar da zaben na raba gardama.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG