Moses mai shekaru 29 bai dade da dawowa Chelsea din ba, bayan zaman da yayi na dan lokaci a kungiyar Inter Milan ta kasar Italiya, wanda ya kare a karshen kakar wasanni da ta gabata.
Tun kafin wannan ma Moses ya yi zaman aro a kungiyar Fenerbahce ta kasar Turkiyya, inda ya buga mata wasanni 20.
To sai dai duk da yake yana da sauran shekara daya a kwantaraginsa da Chelsea, mai horar da ‘yan wasan kungiyar Frank Lampard ya fito fili ya bayyana cewa Moses ba ya cikin tsarinsa a wannan kakar wasanni.
Duk da yake Inter Milan ta kuma yin wani yunkurin na sake karbar Moses a zaman aro, to amma hakan bai samu ba saboda ba’a cimma daidaito ba.
Facebook Forum