Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutune 66 Sun Mutu A Hadarin Jirgin Saman Iran


Wani jirgin saman kamfanin Aseman na Iran
Wani jirgin saman kamfanin Aseman na Iran

Ana wata, ga wata! Bayan faduwar wasu jiragen sama a wasu kasashe kwanan nan, sai kuma gashi wani jirgin Iran ya fadi, har mutane 66 sun riga mu gidan gaskiya.

Wani jirgin saman kasar Iran mai zirga zirga a cikin kasar, ya fado kan tsaunukan Zagros da ke kasar, inda dukkan mutane 66 da ke cikin jirgin su ka mutu.

Jami’an kamfanin jirgin na Aseman sun ce jirgin na dauke ne da matafiya 60, ciki da wani yaro da kuma ma’aikatan jirgin su 6.

Jirgin ya tashi daga birnin Tehran a yau dinnan Lahadi zuwa birnin Yasuj da ke lardin Isfahan, tafiyar kimanin kilomita 560.

Kungiyar agajin Red Crescent ta Iran ta ce ta tura masu kai dauki zuwa wurin, to amma an ce babu kyan yanayi ta yadda ma jirgi mai saukar ungulu ba zai iya sauka kusa da inda aka yi hadarin ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG