Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda PDP Ta Kammala Zabukan Fitar Da Gwani  Na Gwamnoni A Wasu Jihohin Najeriya 


Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi kwanan nan (Twitter/ PDP)

A jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya jam'iyyar ta gudanar da zaben tsayar da dan takarar ta ta hanyar sasanci wanda gwamna Tambuwal ya jagoranta.

SOKOTO, NIGERIA - Babbar jam'iyar adawa ta PDP ta kammala zabukan fitar da ‘yan takararta na gwamnoni a mafi yawa daga cikin Jihohin kasar, inda wadanda aka tsayar ke ta neman hadin kan wadanda suka fadi zabubukan, abin da masana ke ganin yana da wuya saboda a mafiyawan wurare zabukan son rai ne ake yi.

Yanzu dai a iya cewa babbar jam'iyar adawa ta PDP a Najeriya ta shirya domin kare kujerin gwamnonin da ke gare ta a wasu jihohi da kuma karbe wasu kujerin daga wasu jam'iyu da yake ta tsayar da ‘yan takarar gwamna a mafiyawan Jihohin kasar.

Bayan sasantawar, an jefa kuri'a inda aka tsayar da tsohon sakataren gwamnati Sa'idu Umar dan takarar gwamna da dan tsohon gwamna Sagir Attahiru Bafarawa a zaman mataimaki, shi kuwa mataimakin gwamna mai ci yanzu zai tsaya takarar sanata.

Sa'idu Umar, daya daga cikin wadanda aka zaba takarar gwamna ya yi kira ga sauran ‘yan takara da ‘ya'yan jam'iyar akan a hada kai wuri daya a samu nasarar babban zabe.

A jihar Kebbi ma an gudanar da zabukan inda tsohon babban kumandan Sashe na takwas na sojojin Najeriya Shiyar Sokoto, Manjo Janar Aminu Bande Mai ritaya ya samu galaba inda ya doke sauran 'yan takara 4, shi ma dai ya nemi hadin kan abokan karawarsa.

Duba da yadda ake shirya zabukan fitar da ‘yan takarar ne ya sa masu sharhi akan lamurran yau da kullum ke ganin kiran da ake yi na hada kai abu ne da kamar wuya, a cewar Farfesa Bello Badah.

Akasarin zabukan da aka gudanar wasu sun samu damuwa saboda sakamakon ba su zo yadda suke bukata ba, yayin da kuma wasu abin ya yi musu kyau.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Nasir:

PDP Ta Kammala Babban Zabukan Fitar Da Gwani  Na Gwamnoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG