Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Cafke Wanda Ya Kashe Ardon Panyam A Jos


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya dake aikin samar da tsaro a jihar Filato, wato 'Operation Safe Haven', ta damke daya daga cikin wadanda ake zargi da kisan Ardon yankin Panyam a karamar hukumar Mangu, Alhaji Adamu Idris Gabdo.

PLATEAU, NIGERIA - A ranar 24 ga watan Satumban wannan shekara ne, Ardon na Panyam wanda ke gudun hijira a jihar Bauchi, bayan rikicin da ya auku a wassu sassan karamar hukumar ta Mangu, ya gamu da ajalinsa, yayin da wasu mutane suka halaka shi a hanyarsa ta ziyarar 'yan'uwansa a garin Panyam.

Laftanar Kanar Ishaku Takwa, mai magana da yawun rundunar sojoji ta uku dake Jos, ya ce tun bayan da suka sami labarin bacewar Ardon ne, hafsan hafsoshin Najeriya ya basu umurni su nemo Ardon ko da rai ko a mace.

Wanda ake zargi da kisan aka kuma kamo shi, Philip Gukas ya amsa tuhumar da ake yi masa.

A watan Mayu na wannan shekara ne, 'yan bindiga dauke da muggan makamai suka auka wa mutane a cikin dare suka halaka mutane fiye da dari da talatin a kididdigar da hukumomi suka bayar, yayinda wasu kungiyoyi ke ikirarin adadin wadanda aka kashen sun haura dari biyu.

'Yan bindigar sun kuma kona gidaje a kauyuka da dama, yayinda dubban mutane ke gudun hijira.

Ko a farkon wannan mako rundunar sojin ta chapke wassu mutane biyu da take zargi da mallakar wurin kera makamai ba tare da izini ba, a karamar hukumar Jos ta Kudu.

Rundunar ta ce ta sami bindigogi kirar AK-47, da wassu bindigogi da albarusai masu tarin yawa.

Rundunar ta kara da cewa irin wadannan nasarori da take samu zasu kai ga kakkabe dukkan masu haddasa fitina a sassan jihar Filato da bangaren kudancin Kaduna.

Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:

Rundunar Sojin Najeriya Ta Cafke Wanda Ya Kashe Ardon Panyam A Jos.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG