Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Ce Iran Na Aiki da Yarjejeniyar Dakile Shirinta Na Nukiliya


Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson

A wani abu na ba zata sakataren harkokin wajen Amurka ya amsa cewa a zahiri kasar Iran na aiki da yarjejeniyar kasa da kasa da aka yi da ita domin dakile shirinta na nukiliya amma kuma wai shugaban Amurka Donald Trump na bukatar majalisar dokokin kasar ta gyara wasu kurakurai dake tattare da yarjejeniyar

Karshenta dai, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson, jiya Lahadi ya amsa cewa "a aikace," Iran na aiki da yarjajjeniyar kasa da kasa kan dakile shirinta na nukiliya, to amma ya ce Shugaba Donald Trump na son Majalisar Dokokin Amurka ta bullo da abin da ya kira, 'gamsasshiyar dabara" ta gyara abin da shugaba Trump ke ganin wasu kurakurai ne tattare da yarjajjeniyar.

Babban jami'in diflomasiyyar Amurka din ya gaya ma tashar telebijin taCNN cewa Iran, a ta bakinsa, "ta yi kaurin suna wajen yawan alamar kamar zata karya sharuddan yarjajjeniyar ta 2015" wanda hakan ne ya ankarar da Trump wanda ranar Jumma'a ya janye bayar da tabbaci kan salon Iran na kiyaye yarjajjeniyar, don haka ya rage ga Majalisar Dokokin Amurka ta maido da takunkumnin da aka kakaba ma Iran kafin a dage mata su bayan da kulla yarjajjeniya tsakaninta da Amurka da Tarayyar Turai da Faransa da Burtaniya da Jamus da Rasha da kuma China.

To amm Ministan Harkokin Wajen Iran, Javad Zarif, wanda shi ne ya wakilci Iran wurin tattaunawa kan yarjajjeniyar, ya fada a shirin gidan talabijin na CBS na "Face the Nation" cewa watsi da yarjajjeniyar da Trump ya yi zai sa "babu kuma wanda zai sake yarda ya kulla wata yarjejeniya mai tsawon wa'adi da duk wata gwamnatin Amurka saboda tsawon duk wani alkawaria nan gaba don za'a ga cewa, gwarwagon dadewar yarjejeniyar yakan dogara ne akan gwargwadon dadewar gwamnati."

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG