Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Senegal Ta Ce Bata Fidda Tsammani Kan Sadio Mane Zai Shiga Gasar Cin Kopin Duniya Don Ya Samu Rauni.


Sadio Mane of Senegal
Sadio Mane of Senegal

Yayin da ake saura kwanaki 11 a fara gasar cin kopin duniya a Qatar, Senegal ta ce ba zata yi garajen yanke hukunci a kan dan wasanta Sadio Mane da ya samu rauni yayin wasan kungiyarsa ta Bayern Munich a wasan lig din kasar Jamus a jiya Talata cewa ba zai iya yin wasa a gasar cin kopin duniya ba.

Dan wasan gaban ya fice ne yayin da aka yi minti 20 kacal da fara wasa a lig din Bundesliga ta kasar Jamus tsakanin kungiyarsa da Werder Bremen a dandalin Allianz Arena bayan ya samu rauni.

Da sanyin safiyar yau Laraba rahotanni sun nuna cewa da alama tsohon dan wasan Liverpool ba zai iya yin wasa a gasar cin kopin duniya ba sakamakon mummunan rauni da ya samu.

Sadio Mane of Senegal
Sadio Mane of Senegal

Sai dai kungiyar wasan Senegal ta Taranga Lions ta ce tana nazari a kan halin da ake ciki kuma bata fidda tsammani ba a kan zakaran nata.

Jim kadan bayan wasan na jiya da Bremen, hukumar kwallon kafar Senegal da kungiyar Bayern Munich sun tattauna ta wayar tarho, a cewar wani jami’in Taranga Lions yana fadawa manema labarai.

Hukumar kwallon kafar Senegal ta ce ba zata yi gaggawan yanke hukunci ba. “Bamu samu da cikakken bayani game da raunin ba. Sadio mutum ne mai ji da karfi. Mun saurara mu ji yanda zata kaya,” in ji hukumar.

Sadio Mane of Senegal
Sadio Mane of Senegal

Senegal ta kasance a cikin rukuni A a gasar cin kopin duniya, inda zata fafata da Netherlands, Qatar mai masaukin baki da kuma Ecuador.

Babban kocin tawagar kwallon Senegal Aliou Cisse zai gana da ‘yan jarida a ranar Juma’a 11 ga wannan watan Nuwamba, domin ya fitar da jerin sunaye na karshe na ‘yan wasa 26 da zasu yiwa Senegal wasa a gasar cin kopin duniya a Qatar.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG