Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekaruna Sun Ja, Ina Fatan Na Gama Lafiya Don Na Je Na Huta - Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin ziyarar aiki da kai London (Facebook/Femi Adesina)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin ziyarar aiki da kai London (Facebook/Femi Adesina)

"Yin aikin sa’a 6, 7 zuwa 8 kullum a ofis ba wasa ba ne.” Buhari ya ce.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana fatan ya kammala ragowar watanni 17 da suka rage masa lafiya don ya je ya huta.

Cikin wata hira da ya yi ta musamman da gidan talabjin na kasa NTA a ranar Alhamis kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito, Buhari ya ce shekarunsa sun ja kuma suna nunawa.

“Akwai sa’o’ina suna can suna hutawa, ina mai tabbatar maka cewa, ina fatan ni ma nan da wata 17 ayyuka za su ragu min.”

“Shekaruna sun ja suna kuma nunawa, yin aikin sa’a 6, 7 zuwa 8 a kullum a ofis ba wasa ba ne.” Muhammadu Buhari ya fada a hirar.

Shugaban ya ce irin ayyukan da yake gudanarwa sun hada da taron majalisar zartarwa da ake yi a duk mako, duba rahotanni daga jihohi da dama wadanda ake yi ta yanar gizo.

A ranar 17 ga watan Disamba Muhammadu Buhari ya cika shekara 79 da haihuwa, hakana na nufin zai kammala wa’adinsa na karshe yana da hekara 80.

Ziyarar Shugaba Buhari a Kasar Turkiyya
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:38 0:00

Ziyarar Shugaba Buhari a Kasar Turkiyya

Najeriya Ta Kaddamar Da Jiragen Yaki Na Ruwa Da Jirage Masu Saukar Ungulu Don Yaki Da Masu Fashi A Teku
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:39 0:00

Najeriya Ta Kaddamar Da Jiragen Yaki Na Ruwa Da Jirage Masu Saukar Ungulu Don Yaki Da Masu Fashi A Teku

XS
SM
MD
LG